Kamala Harris kenan take karɓar gaisuwa daga yara a Ghana ranar 23 ga watan Maris na 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamala Harris kenan take karɓar gaisuwa daga yara a Ghana ranar 23 ga watan Maris na 2023
  • Marubuci, By Andrew Webb
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Bayan ya fice daga neman takarar shugabancin Amurka, Joe Biden ya mara wa mataimakiyarsa Kamala Harris baya don ta maye gurbinsa.

Har yanzu ba a zaɓeta ba a matsayin ‘yartakara a hukumance a jam’iyyar Democrat, amma idan ta yi nasarar cin zaɓen za ta zama mace ta farko shugabar Amurka kuma wadda ke da tsatson Indiya da ƙasar Jamaika.

Kuma za ta zama shugaba ta farko tun bayan Andrew Jackson – a 1829 – ‘yar ‘yan-cirani.

Ga wani nazari da muka yi game da ƙwarewar Kamala Harris a fannin alaƙa da ƙasashen duniya, da kuma irin ra’ayinta kan wasu lamurra na manufofin Amurka kan ƙasashen wajen.

Kamala Harris da mijinta Douglas Emhoff suke sumbatar juna yayin yaƙin neman zaɓenta a Wilmington na jihar Delaware

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kamala Harris da mijinta Douglas Emhoff suke sumbatar juna yayin yaƙin neman zaɓenta a Wilmington na jihar Delaware

Ukraine

Ɗaya daga cikin manyan manufofin ƙasashen waje da Kamala Harris da kuma ‘yan jam’iyyar Republican za su samu saɓani a kai shi ne batun yaƙin Rasha da Ukraine.

Ra’ayin Trump kan yaƙin na tayar da hankalin ƙasashen da ke goyon bayan Ukraine.

Wasu ƙasashen Yamma na fargabar idan Trump ya ci zaɓen zai rage ƙarfin goyon bayan da Ukraine ɗin ke samu kuma ya ƙarfafa wa Rasha gwiwar ci gaba da samun nasara.

A bayyane, Harris ta goyi bayan matakan Biden na tura wa Ukraine makamai a yaƙin tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa ƙasar a 2022.

Ta jagoranci tawagar Amurka zuwa taron harkokin tsaro da aka yi a birnin Munich na Jamus a 2022, ‘yan makonni kafin motocin yaƙin Rasha su afka wa Ukraine ɗin.

A watan Yunin 2024, ta wakilci Amurka taron neman zaman lafiya a Ukraine da aka yi a Switzerland.

Kamala Harris take gaiswa da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a watan Yunin 2024 yayin taron Switzerland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamala Harris take gaiswa da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a watan Yunin 2024 yayin taron Switzerland

Sai dai kuma, a kowane lokaci tana tare da rakiyar jami’an da ke da ƙwarewa sosai a fannin ƙasashen waje, kamar Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken, da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan.

Kamala ba ta taɓa zuwa Ukraine ba, amma ta gana da shugaban ƙasar sau shida.

Kamala Harris (hagu) da Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi (tsakiya) riƙe da tutar Ukraine yayin da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi wa Majalisar jawabi a watan Disamban 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kamala Harris (hagu) da Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi (tsakiya) riƙe da tutar Ukraine yayin da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi wa Majalisar jawabi a watan Disamban 2022

Fargabar da ƙasashen Yamma ke yi ita ce cewa Trump zai iya tilasta wa Ukraine ta haƙura da yankunan da Rasha ta ƙwace mata domin kawo ƙarshen yaƙin.

Rasha da Nato

Kamala Harris ta ci alwashin cewa Amurka ba za ta taɓa gazawa ba wajen cika alƙawuran da ta ɗauka game da ƙawancen ƙasashe na tsaro watau Nato – wanda ya ƙunshi ƙasashen Turai da kuma na Arewacin Amurka.

Ta sha sukar Mista Trump game da barazanar da ya dinga yi ta janye Amurka daga ƙawancen idan sauran ƙasashen suka gaza ba da aƙalla kashi biyu cikin 100 na jimillar arzikin da suke samu a cikin gida.

Trump ya ce zai ƙarfafa wa Rasha Nato gwiwar ta mamaye duk ƙasar Nato da ta ƙi biyan kashi biyun cikin 100 da ya kamata ta bayar.

“Indai har wani tsohon shugaban Amurka zai ce zai ba wa ɗan kama-karya damar mamaye ƙawayenmu kuma Amurka na kallo – babu wani shugaban Amurka a tarihi da ya taɓa sassauta wa shugaban na Rasha,” a cewar Kamala.

Kamala kenan take yi wa magoya bayanta jawabi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kamala kenan take yi wa magoya bayanta jawabi

Isra’ila da yaƙin Gaza

Kamala ta goyi bayan Isra’ila a fili, tana mai cewa ƙasar na da ‘yancin kare kanta daga Hamas bayan harin 7 ga watan Oktoban 2023.

“Ba za mu saka wani sharaɗi ba game da goyon bayan da muke bai wa Isra’ila wajen kare kan ta,” kamar yadda ta faɗa a Nuwamban 2023.

Amma wata ɗaya bayan haka, ta nuna kakkausar ra’ayi game da Isra’ila sama da na Biden da sauran jami’an gwamnatin Amurka, inda ta ce “an kashe Falasɗinawa masu yawa” a hare-haren Isra’ila kan Hamas a Gaza.

“Dole ne Isra’ila ta ƙara ƙaimi wajen kare rayukan fararen hula,” a cewarta.

Jami'ar Texas ta Austin na cikin makarantun da suka fuskanci zanga-zangar ƙin jinin yaƙin Gaza da karaɗe jami'o'in Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jami’ar Texas ta Austin na cikin makarantun da suka fuskanci zanga-zangar ƙin jinin yaƙin Gaza da karaɗe jami’o’in Amurka

Zuwa watan Maris na shekarar nan, bayan zanga-zanagr da ta karaɗe jami’o’in Amurka kan yaƙin na Gaza, Kamala ta ce “dole ne Isra’ila ta yawaita kayan agajin da ake shigarwa Gaza – babu wani uzuri”.

Mista Trump ya nuna goyon baya sosai ga Isra’ila a wa’adin mulkinsa na farko. Ya bayyana goyon bayan Amurka ga Isra’ila ta yi amfani da birnin Ƙudus a matsayin babban birninta lokacin da ya kai ziyara.

Sau biyu Kamala tana zuwa Gabas ta Tsakiya a matsayinta na mataimakiyar shugabar ƙasa, amma ba ta je Isra’ila ba – idan aka kwatanta da Trump wanda ya je yana kan mulki.

Wasu Falasɗinawa kenan suke dudduba ɓaraguzai bayan wani harin Isra'ila a yankin Al-Zawaida da ke tsakiyar Zirin Gaza ranar 19 ga watan Yulin 2024

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu Falasɗinawa kenan suke dudduba ɓaraguzai bayan wani harin Isra’ila a yankin Al-Zawaida da ke tsakiyar Zirin Gaza ranar 19 ga watan Yulin 2024

Nahiyar Amurka ta Tsakiya

Ɗaya daga cikin ayyukan Kamala a matsayinta na mataimakiyar shugabar ƙasa shi ne daƙile dalilan da ke jawo baƙin haure shiga ƙasar daga Mexico.

Mista Trump da sauran ‘yan Republican sun sha sukar ta kan batun, suna cewa ta gaza kare iyakokin ƙasar.

Kamala Harris kenan take ɗaga hannu bayan isarta filin jirgi na Aeropuerto La Aurora na ƙasar Guatemala a watan Yunin 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamala Harris kenan take ɗaga hannu bayan isarta filin jirgi na Aeropuerto La Aurora na ƙasar Guatemala a watan Yunin 2021

Lokacin da wani ɗanjarida ya tambaye ta game da dalilin da ya sa ba ta taɓa kai ziyara kan iyakar Amurka da Mexico ba, amsar da ta bayar ta jawo mata tsokana daga ‘yan’dawa.

Kamala ta ce: “Kada ku zo. Kada ku zo. Amurka za ta cigaba da tabbatar da dokoki a kan iyakarta. Idan kuka zo iyakarmu, za a mayar da ku.”

Kamala kenan lokacin da take jawabi a Guatemala City ranar 7 ga watan Yuni

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamala kenan lokacin da take jawabi a Guatemala City ranar 7 ga watan Yuni

Sai kuma ta kai ziyara kan iyakar lokacin da ta yi balaguro zuwa Texas a watan Yunin 2021.

Masu neman mafaka a Amurka ne nan suke kan hanyar zuwa ganawa da jami'an hukumar kwastam na Amurkar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Masu neman mafaka a Amurka ne nan suke kan hanyar zuwa ganawa da jami’an hukumar kwastam na Amurkar

Daƙile baƙin haure daga Mexico babbar manufa ce ta Trump bayan da ya sha yin alƙawarin gina katanga a kan iyakar a 2016.

Rahotonni sun ce yawan baƙin hauren da ke shiga sun ƙara yawa sosai a 2021, 2022, 2023 – lokutan da Kamala ke kan mulki kenan.

Sun ragu a watan Yuni lokacin da Shugaba Biden ya saka hannu kan wani umarnin shugaban ƙasa da ya hana wasu da yawa neman mafaka a ƙasar.

Magoya bayan Kamala Harris

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Magoya bayan Kamala Harris

China

Kamar Trump, Kamala na yawan sukar China. Amma ta fi mayar da hankali kan siyasa sama da kasuwanci – saɓanin Trump.

Ta zargi China da “tsangwamar” maƙwabtanta a Tekun Kudancin China.

Tsibirin Cay, wanda aka sani da Tsibirin Spratly, Vietnam ce ke iko da shi amma kuma China na taƙaddama kan mallakarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsibirin Cay, wanda aka sani da Tsibirin Spratly, Vietnam ce ke iko da shi amma kuma China na taƙaddama kan mallakarsa

Kamala Harris ta taɓa ziyartar kan iyakar da ta fraba Koriya ta Kudu da ta Arewa a watan Satumban 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kamala Harris ta taɓa ziyartar kan iyakar da ta raba Koriya ta Kudu da ta Arewa a watan Satumban 2022

Lokacin da Trump ya kai irin wannan ziyarar a 2019 ya tsallaka ɓangaren Koriya ta Arewa, inda ya gaisa da Kim Jong-un.

Ya kuma tattauna da Kim ɗin a Singapore.

Donald Trump ya gaisa da Shugaban Koriya ta Kudu Kim Jong-un bayan ya tsallaka iyakar da ta raba Koriyoyin biyu a watan Yunin 2019

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Donald Trump ya gaisa da Shugaban Koriya ta Kudu Kim Jong-un bayan ya tsallaka iyakar da ta raba Koriyoyin biyu a watan Yunin 2019

Afirka da Gabas ta Tsakiya

A 2023, Kamala na cikin jami’an gwamnatin Amurka da suka ziyarci Afirka.

Yunƙurin na nufin aniyar gwamnatin Amurka na ƙara yauƙaka alaƙa da ƙasashen Afirka yayin da take fuskantar ƙalubale daga sauran manyan ƙasashen duniya kamar Rasha da China.

A watan Mayun 2024, ta sanar da shirin taimaka wa ƙasashen ninka yawan layin intanet da kashi 80 cikin 100 tsakanin al’ummarta.

Kazalika, Kamala na cikin tawagar da ke ƙoƙarin rage kaifin da Saudiyya ke yi a Yemen.

Lokacin da take sanata, Kamala ta hana sayar wa Saudiyya makamai saboda yaƙin da take yi a Yemen ɗin da kuma kisan ɗanjarida Jamal Khashoggi a Turkiyya.

Amurka na zargin Saudiyya da kisan ɗanjarida Jamal Khashoggi

Asalin hoton, Middle East Monitor handout via Reuters

Bayanan hoto, Amurka na zargin Saudiyya da kisan ɗanjarida Jamal Khashoggi

‘Yancin ɗan’adam

Baya ga rage wa Saudiyya kayan aiki, Kamala ta goyi bayan kafa dokokin da za su taimaka wa kare haƙƙin ɗan’adam a wasu wuraren.

Ta goyi bayan dokar da za ta ba da damar tunawa da kisan ƙare-dangi a Armenia, lamarin da ke jawo cecekuce tsakaninta da Tukriyya wadda ƙawarta ce a ƙungiyar ƙawance ta Nato tsawon shekara 100.

Kamala ta kuma goya wa yunƙurin dakatar da Iran daga mallakar makamin nukilya a 2015.

Masu zanga-zanga ne riƙe da hoton Qassem Soleimani bayan Amurka ta kashe shi a Iraƙi yayin wani hari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga ne riƙe da hoton Qassem Soleimani bayan Amurka ta kashe shi a Iraƙi yayin wani hari

Ta kuma yi tir da harin da Amurka ta kai lokacin gwamnatin Trump a 2020 da ya kashe janar ɗin Iran Qassem Soleimani a Syria.

Daga baya ma ta goyi bayan wani yunƙuri da bai yi nasara ba da ya so ya hana ci gaba da kai wa jagororin Iran hari.