abubuwan-da-ke-faruwa-a-najeriya-da-sassan-duniya

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Netanyahu na shirin korar ministan tsaron cikin gida

    Kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun ce Firaiministan ƙasar Benyamin Netanyahu yana shirin korar ministan tsaron cikin gida, Yoav Gallant nan take.

    Rahotannin sun ce Gideon Sa’ar na ƙawancen United Right ne zai maye gurbin Mista Gallant – wani abu da ofishin Netanyahu ya musanta.

    An shafe tsawon watanni ana yaɗa jita-jita game da rashin jituwar da ke tsakanin Mista Gallant da Netanyahu game da mamayar da aka yi a kudancin Lebanon domin daƙile hare-haren dakarun Hezbollah.

    Tun farko, ministan tsaron Isra’ila, Itamar Ben-Gvir ya ce dole ne a cimma matsaya game da iyakar arewacin Isra’ila sannan ba Mista Gallant ne mutumin da ya dace wajen jagorantar aikin ba.

  3. Duniya ta ba mu kunya saboda kasa taimakon mutanen Gaza – MDD

    Gaza

    Asalin hoton, United Nations

    Babbar jami’iar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sa ido kan agaji da sake gina Gaza ta shaida wa BBC cewa ɗaukacin ƙasashen duniya sun kasa ceto fararen hular da ba su ji ba su gani ba a yankin Gaza kan halin da suke ciki.

    Sigrid Kaag, wadda aka naɗa watanni tara da suka gabata don inganta yadda ake kai kayan agajin da ake buƙata cikin gaggawa, ta ce rahoton da za ta bai wa kwamitin tsaro na MDD a yau Litinin zai kasance “mai matukar damuwa”.

    Ta kwatanta halin da ake ciki a yankin a matsayin “babban bala’i”.

    “Ba za mu iya cimma abin da muke buƙata ba, balle a samar da fata mai kyau ga fararen hula a Gaza,” in ji ta.

    Ta ce Gaza shi ne wuri mafi haɗari na aiki a duniya a yanzu.

    Ta nuna ɓacin rai cewa ba za a iya shawo kan al’amura a yankin ba, ba tare da an tsagaita wuta da kuma sakin Isra’ilawa da aka yi garkuwa da su ba.

  4. Zan tsaya don ganin ƴan sandan tabbatar da ɗa’a ba su takurawa mata ba – Shugaban Iran

    Masoud Pezeshkian

    Asalin hoton, Reuters

    Sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya ce zai yi amfani da ikonsa wajen ganin cewa ƴan sandan tabbatar da ɗa’a ba su takurawa mata ba.

    Yana tattaunawa ne da ƴan jarida yayin da aka cika shekara biyu da mutuwar matashiya Mahsa Aminu wadda aka kama saboda karya dokar sanya hijabi.

    Wata ƴar jarida ta shaida wa Mista Pezeshkian cewa dole ta sa ta bi hanyoyi daban-daban domin kaucewa jami’an tabbatar da ɗa’a a ƙoƙarinta na zuwa taron manema labaran.

    Shugaban ya mayar da martani da cewa bai kamata ƴan sandan su riƙa tunkarar mata ba inda ya yi alƙawarin bibiyar batun.

    An yi ta yaɗa bidiyon wannan tattaunawar a shafukan sada zumunta.

  5. Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu tare da cinna wa ofishinsu wuta a Anambra

    Ƴan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun ƙona ofishin ‘yan sanda na Umunze da ke karamar hukumar Orumba ta Kudu a jihar Anambra tare da kashe ‘yan sanda biyu.

    Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari ne a ofishin ‘yan sandan tare da amfani da ababen fashewa, inda suka yi ta harbe-harbe, yayin da wani ɓangare na ofishin ke ci da wuta.

    An ruwaito cewa harin ya yi sanadiyar mutuwar jami’an ‘yan sanda biyu da ke bakin aiki a lokacin da suka yi ƙoƙarin tinkarar maharan.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin ‘yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, na tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an gano gawawwakin ‘yan sandan da suka rasu, an kuma garzaya da su ɗakin hutu a asibiti.

    Ya kuma ƙara da cewa jami’an tsaro na haɗin gwiwa da suka haɗa da ‘yan sanda da sojojin ƙasa da na ruwa da na Civil Defence da kuma sauran hukumomi, sun gano wasu abaubuwan fashewa guda biyar da ba su kai ga tashi ba, kuma suna bin tsawun ƴan bindigar domin cimmu su.

  6. Tinubu ya kai ziyara Maiduguri don jajantawa al’umma iftila’in ambaliya

    Ambaliya

    Asalin hoton, Gamnatin Najeriya

    Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara birnin Maiduguri domin jajantawa al’ummar jihar Borno iftila’in ambaliyar da ya afka musu.

    Ziyarar tasa na zuwa ne kwanaki shida bayan mummunar ambaliyar da birnin ya fuskanta wanda rabon a ga haka tun bayan shekara 30 da suka wuce.

    Bayan isarsa birnin, kai-tsaye ya garzaya ɗaya daga cikin sansanonin da aka tsugunar da waɗanda lamarin ya ɗaiɗaita domin jajanta musu.

    Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tallafawa mutanen.

    “Ina son tabbatar muku da cewa za mu tallafa muku domin rage raɗadin da kuka shiga sakamakon wannan iftila’i,” in ji Tinubu.

    Daga bisani, Tinubu ya ziyarci fadar Mai Martaba Shehun Borno, Alh Umar Garbai Ibn El-Kanemi tare da rakiyar gwamna Babagana Zulum domin jajantawa Basaraken kan al’amarin da ya faru.

    Ambaliya

    Asalin hoton, Gamnatin Najeriya

    Tawagar shugaban da ta kai ziyara birnin na Maiduguri ta kunshi shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ministan aikin gona Abubakar Kyari da kuma sauran mukarrabai da masu taimaka masa.

    Ɓallewar madatsar ruwa ta Alau da ke wajen birnin ce ta haifar da mummunar matsalar.

    Ambaliyar ta rutsa da mutum 37 a cewar hukumar ba da agaji ta ƙasa Nema.

    Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta ce ta yi sanadiyar ɗaiɗaita mutane sama da miliyan ɗaya.

  7. An samu raguwar hauhawar farashi a watan Agusta – NBS

    Farashin kayayyaki

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce an samu raguwar hauhawar farashi a ƙasar daga kashi 33.40 a watan Yuni zuwa kashi 32.15 a watan Agusta.

    A cewar wani rahoto da NBS ɗin ta fitar ranar Litinin, ta ce an samu raguwar ta kashi 32.15 ne a watan Agustan 2024, yayin da farashin abinci kuma ya kasance a kashi 37.52 a watan na Agusta.

    “Alkaluman da muka tattara sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.25 idan aka kwatanta da n watan Yulin 2024,” in ji rahoton.

    NBS ta ce farashin kayan abinci a watan Agustan 2024 ya kai kashi 37.52, idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Agustan 2023 na kashi 29.34.

    Ta ce an samu hauhawar farashin kayan abincin ne sakamakon tashin farashin kayayyaki kamar burodi da masara da hatsi da dawa da dankalin turawa da rogo da dabino da sauransu.

    Hukumar ta ce farashin abinci a watan Agustan 2024 ya kasance a kashi 2.37 wanda ya nuna raguwa da kashi 0.10 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Yulin 2024 na kashi 2.47.

    Ta ce za a iya danganta raguwar da faɗuwar farashin kayayyaki kamar sikari da ganyen shayi da man gyaɗa da madara da dawa ganyayyaki da sauransu.

  8. Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga al’ummar Zamfara kan hatsarin kwale-kwale

    Hatsarin kwale-kwale

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Bola Tinubu ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga gwamnati da kuma al’ummar jihar Zamfara kan haɗarin kwale-kwale da ya rutsa da wasu manoma sama da 40 a a karamar hukumar Gummi, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona.

    Wata sanarwa da kakakin shugaban Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban bai ji ɗadin lamarin da ya afku ba.

    Shugaban Najeriyar ya yi alkwarin bayar da tallafi ga waɗanda lamarin ya rutsa da ƴan uwansu.

    “Shugaba Tinubu ya bai wa hukumomin bayar da agaji da su gaggauta gudanar da bincike kan batun kifewar kwale-kwalen da kuma ambaliya da aka samu a yankin domin tallafawa mutane,” in ji sanarwar.

    Ya kuma umarci hukumomin da su yi aiki tare da gwamnatin jihar ta Zamfara domin ganin yadda za a tallafawa mutanen da abin ya shafa.

  9. Majalisar Wakilai za ta yi bincike kan batun sojan ruwa Seaman Abbas

    ..

    Asalin hoton, Gagdi/X

    Kwamitin sojin ruwa na majalisar wakilan Najeriya ya ce zai yi bincike dangane da tsare sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna na tsawon shekaru shida ba “bisa ƙa’ida” ba.

    Wata sanarwa da shugaban kwamitin, Yusuf Adamu Gagdi ya wallafa a shafinsa na X, ta ce “an tsare Seaman Abbas Haruna ne bisa umarnin wani babban soja Birgediya Janar M.S Adamu. Saboda haka kwamitin zai bincika domin tabbatar da cewa duk waɗanda ke da hannu a al’amarin sun fuskanci hukunci daidai abin da suka aikata.”

    Yusuf Gagdi ya ƙara da cewa “rashin imanin da aka nuna a kan sojan ruwan saboda ɗan saɓanin da aka samu tsakaninsa da babbansa ya sa mutane da dama sun zubar da hawaye a lokacin da mai ɗakinsa ke bayar da bahasin yadda a al’amarin ya faru a gidan rediyo da talbijin na Brekete.”

    Da ma dai hedikwatar tsaron Najeriya ma ta ce ta ga wani bidiyo da ke yawo na zargin tsare wani sojan ruwa mai suna Seaman Abbas Haruna tsawon shekaru shida kuma tana bincike a kai.

    Hedikwatar rundunar tsaron ta Najeriya a wata sanarwa mai sa hannun kakainta, Birgediya Janar Tukur Gusau ta “muna bai wa al’ummar Najeriya tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya a shirye take ta samar da adalci da daidaito bisa dokokin ƙasa.

  10. Haɗaddiyar Daular Larabawa ta ba Najeriya agajin abinci sakamakon ambaliya

    ..

    Asalin hoton, UGC

    Rahotanni na cewa Haɗaddiyar Daular Larabawa, (UAE) ta bai wa Najeriya taimakon abinci tan 50 domin tallafa wa waɗanda ambaliar ruwa ta ɗaiɗaita.

    Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta NEMA, Manzo Ezekial a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin ya ce ambasadan UAE, Salem Alshami ya miƙa kayan tallafin ga hukumar.

    Ambasadan ya shaida cewa tallafin ya samu ne sakamakon kuɗurin shugaban UAE, Sheikh Mohammed Al Nahyan na ganin ya tallafa wa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya faɗawa.

    Manzo ya ce manyan jami’an hukumar NEMA da ma’aikatar ƙasashen waje da kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

  11. Masu bikin Mauludi 40 sun rasu sakamakon haɗarin mota a Kaduna

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanai daga jihar Kaduna sun ce aƙalla mutum 40 ne masu Mauludi suka rasu da yammacin ranar Lahadi, sakamakon wani haɗari inda wata babbar motar kaya ta hau kan wata mota ƙirar J5 ɗauke da mutum fiye da 70.

    Wani wanda ɗaya ne daga masu shirya Mauludin ya shaida wa BBC cewa “daga garin Kwandari za su zo nan Saminaka a daidai Lere kan kwana wata babbar mota ta hau kan motarsu. An ce wani mai babur ne ya gifta wa direban babbar motar inda shi kuma mai babbar motar ya kauce masa abin da ya sa ya hau kan motar masu Mauludin.”

    Bayanan sun ce aƙalla mutum 30 ne suke a asibiti inda suke samun kulawa.

    Wani wanda shi ne mutumin da ya ɗauki alƙaluma bayan haɗarin ya ce “waɗanda suka mutu su 41 ne mata guda 19 da ƙananan yara 10 da sauran mutane musamman tsaffi kusan 11 sai kuma masu rauni fiye da 30.”

  12. Jamus za ta ƙara tsaurara bincike a kan iyakokinta na yammaci

    Jamus na shirin tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinta ta yankin arewaci da yammacin kasar.

    Za a rinƘa bincikeN motocin da ke tsallakowa iyakar Ƙasar ta Denmark da Netherlands da kuma Faransa.

    Wannan kusan irin matakan da take ɗauka kenan a yankunan ƙasashen da ta haɗa iyaka da su ta yankin kudanci da gabashin kasar.

    Gwamnati dai ta ce tana ɗaukar waɗannan matakai ne domin sake inganta tsaron ƙasa. Sai dai tana fuskantar suka daga waɗanda ke ganin tsarin nata na neman cin karo da dokokin Schengen na ƙetarawa ko shiga ƙasashen Turai.

  13. Wane ne Ryan Wesley Routh, mutumin da ake zargi da yunƙurin kisan Trump?

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Kafafen watsa labaran Amurka dai sun bayyana Ryan Wesley Routh a matsayin wanda ake zargi sakamakon yunƙurin kisan ɗantakarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican, Donald Trump, a Florida.

    Mista Routh, mai shekara 58 dai ɗan North Carolina ne inda ya shafe fiye da rabin rayuwarsa a can kamar yadda bayanai masu inganci suka nuna, sai dai kuma a baya-bayan nan ya koma Hawaii da zama.

    Abin da ya aikata ya sanya ana bincike kansa kuma wani abu da ya fito fili shi ne cewa yana da aƙida sosai ta ƙaunar Ukraine. Sannan ya yi shari’u da dama da jama’a.

    Ana dai zargin Ryan da zuwa filin wasan ƙwallon Golf da ke Florida ranar Lahadi, yana ɗauke da bindiga ƙirar AK-47.

    Jami’an FBI sun karɓi bindigar da kuma jakunkuna guda biyu na goyawa a baya daga dajin da ake zargin ɗanbindigar ya ɓoye su.

    Duk da cewa Routh ya tsere a motarsa, amma wani wanda ya shaida al’amarin ya gano shi bayan ɗaukar hotonsa a cikin baƙar motarsa ƙirar Nissan.

    Daga nan ne aka fitar da hoton motar ana neman ta. Ƴansandan yankin sun ce jami’ansu sun gano motar miniti 45 bayan faruwar al’amarin kuma suka bi ta.

    Kuma daga ƙarshe an tsayar da shi a kan babban titin Interstate 95 inda aka tafi da shi domin tsarewa.

  14. Ana ƙara samun yawan waɗanda suka mutu sakamakon ambaliya a Turai

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Alƙaluman mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar da ta afka wa tsakiyar Turai sun ƙaru inda aka fi samun masu mutuwar a ƙasar Czech Republic da Poland da Austria.

    A Czech Republic wani mutum ya nutse a wani kogi da ke kusa da garin Bruntal a arewa maso gabashin ƙasar, sannan mutum bakwai sun yi ɓatan dabo.

    Mutum huɗu ne rahotannin suka nuna sun mutu a ƙasar Poland duk da cewa maimagana da yawun ma’aikatar cikin gidan ƙasar ya ce za a yi bincike domin gano musabbabin mutuwar.

    A Austria kuwa, mutum biyu ne suka mutu da suka haɗ da ɗan shekara 70 da 80 a arewa maso gabashin ƙasar. Ɗaya daga cikin su mazaunin garin Hobersdorf ne wanda ruwan ya ci shi a lokacin da yake fafutukar kore ruwan daga gidansa kamar yadda kafafen watsa labaran Austria suka rawaito.

  15. Ƙasashen duniya sun nuna gazawa wajen tallafa wa al’ummar Falasɗinawa – MDD

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Babbar jami’a a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sa ido kan agaji da sake gina Gaza ta ce duniya ta nuna gazawa wajen taimaka wa fararan hula kusan shekara guda na yaƙi.

    Sigrid Kaag ta faɗa wa BBC cewa rahotan da take shirin gabatar wa kwamitin tsaro na Majalisar a yau Litinin na tattare da labaran ƙunci da tashin hankali.

    An dai naɗa Sigrid Kaag wannan muƙamin ne watanni tara da suka gabata domin inganta yadda ake shigar da agaji Gaza.

    Ta ce a yanzu komai ya tsaru, sai dai kuma ƙoƙarin kare ayarin motocin agaji ya gaza. Ms Kaag ta ce ba ta ganin za a samu wani sauyi a yanzu, indai ba tsagaita wuta aka yi ba.

  16. ‘Za mu tabbatar an yi bincike na adalci kan batun Seaman Abbas’

    ..

    Asalin hoton, Brekete Family

    Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ta wani bidiyo da ke yawo na zargin tsare wani sojan ruwa mai suna Seaman Abbas Haruna tsawon shekaru shida.

    Hedikwatar rundunar tsaron ta Najeriya a wata sanarwa mai sa hannun kakainta, Birgediya Janar Tukur Gusau ta “muna bai wa al’ummar Najeriya tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya a shirye take ta samar da adalci da daidaito bisa dokokin ƙasa.

    Shari’a a kotun soji duk da dai yana ɗaukar lokaci amma tana tabbatar da adalci kamar yadda tsarin aikin soji ya tanada.”

    Sanarwar ta ƙara da cewa a wani martani ga wannan zargi, babban hafsan sojin ƙasar, Janar Christopher Musa ya ba da umarnin fara binciken gaggawa domin gano haƙiƙanin abin da ya faru kuma za a sanar da ƴan ƙasa sakamakon binciken.

    “Muna bai wa ƴan Najeriya tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya za ta tabbatar da an gudanar da bincike kan al’amarin ba tare da ɓata lokaci ba kuma za a gudanar da binciken a faifai.” In ji sanarwar.

    A makon da ya gabata ne dai mai ɗakin Seaman Abbas ta je gidan rediyo na Human Rights Radio da aka fi sani da Brekete Family a Abuja, inda ta bayyana irin halin da maigidan nata yake ciki tsawon shekaru shida a hannun rundunar sojin saman Najeriya.

    ..

    Asalin hoton, DEFENCE HEADQUATERS

  17. Fursunoni mata na yajin ƙin cin abinci a Iran domin tuna wa da Mahsa Amini

    Shekara biyu bayan mutuwar wata matashaiya Baƙurdiya a Iran wadda ‘yan sanda suka kama kan sanya sutura mara da’a, sama da fursunoni mata 30 a gidan yarin Tehran na tuna wa da wannan rana ta hanyar shiga yajin ƙin cin abinci.

    Fitattun masu fafutika da masu adawa da matakan gwamnati, ciki har da Narges Mohammadi da ta lashe kyautar Nobel — na cikin wadanda suka shiga wannan yajin a gidan yarin Evin.

    Mahsa Amini mai shekara 22 an kamata ne kan laifin karya dokokin sanya sutura a Iran.

    Kuma ana da yaƙinin cewa ta mutu ne a hannun jami’an tsaron na Iran, yanayi da ya tunzura ƙazamar zanga-zanga a faɗin ƙasar a wannan lokaci.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Yadda rundunar sojin saman Najeriya ke jigilar tallafin abinci zuwa Maiduguri

    ..

    Asalin hoton, NAF

    Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta fara jigilar kayan tallafin abinci zuwa birnin Maiduguri sakamakon ambaliyar da ta ɗaiɗaita mutum fiye da miliyan biyu.

    Tallafin kayan abincin dai ya samu ne daga hukumar hana fasaƙauri ta Najeriya wato Customs.

    Rundunar sojin saman ta ce a ranar Asabar ta fara kai kayan Maiduguri inda jiragenta suka kai shinkafa buhu 300 masu nauyin kilogram 50 kowanne, a zangon farko.

    Rundunar ta kuma ƙara da cewa tuni da ma ta fara ayyukan bayar da magani ga waɗanda ba su da lafiya.

    ..

    Asalin hoton, NAF

    ..

    Asalin hoton, NAF

    ..

    Asalin hoton, NAF

    ..

    Asalin hoton, NAF

    ..

    Asalin hoton, NAF

  19. Man Ɗangote zai fi tsada a jihar Borno da kewaye kamar yadda NNPCL ya fitar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin mai na Najeriya, NNPC Ltd ya fitar da jadawalin farashin man da ya sayo daga matatar man Ɗangote, a gidajen mai na NNPC a faɗin ƙasar kamar haka:

    • Legas – N950.22
    • Oyo – N960.22
    • Rivers – N980.22
    • Sokoto – N999.22
    • Kano – N999.22
    • Kaduna – N999.22
    • FCT – N999.22
    • Borno – N1,019.22

    ..

    Asalin hoton, NNPCL

  20. Ina cikin ƙoshin lafiya bayan sake yunƙurin kashe ni – Donald Trump

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban Amurka kuma ɗAntakarar sake neman kujerar, Donald Trump ya ce yana nan kalau kuma komai lafiya bayan hukumar bincike ta FBI ta sanar da cewa an yi yunƙurin kashe shi.

    Wakiliyar BBC ta ce, wani jami’in tsaron sirri ne ya hango kan bindiga ya leƙo daga cikin jeji a inda tsohon shugaban ke shaƙatawa a gidansa na Florida, tazarar mita 700 daga inda yake buga ƙwallon golf.

    Nan take jami’in ya yi harbi. Ɗan bindigar da ake zargi ya tsere, amma daga bisani an kamo shi. ‘Yan sanda sun bincike gidansa da ke North Carolina.

    Shugaba Joe Biden da mataimakiyarsa, Kamala Harris, sun nuna matukar jinɗaɗin cewa babu abin da ya sami mista Trump.

    An tsaurara matakan tsaron ɗan takarar shugabancin Amurkar na jam’iyyar Republican tun bayan wani yunƙurin na hallaka shi a watan Yuli.

    Kafar yaɗa labaran Amurka ta bayyana wani mutum mai shekara 58 mai suna Ryan Routh a matsayin wanda ake zargi da yunƙurin kashe Donald Trump.

    Wakilin tashar CBS Cristian Be-na-vides ya ce, bayanan da aka tattara a kansa a shafin sada zumunta, sun nuna cewa yana taimaka wa sojojin haya daga ketare shiga Ukraine a yakinta da Rasha.

    Hotunan bidiyo sun nuna shi ya je Ukraine a kwanan nan. Rashin nuna wani cikakken goyon bayan Donald Trump kan yaƙin Ukraine ya fito ƙararra a gangamin yaƙin neman zaɓensa.

    Akwai kuma saƙonnin nuna goyon-baya ga Falasdinu da Taiwan da China a shafin mutumin da ake zargi

    ..

    Asalin hoton, Newsweek

    Bayanan hoto, Mutumin da ake zargi da yunƙurin kisan Donald Trump na da alaƙa da ƙasar Ukraine