Vladimir Putin yana zantawa da manema labarai kafin taron na Brics

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fadar shugaban ƙasar Rasha ta ce taron da za a yi yana cikin “manyan” da aka taɓa yi a Rasha
  • Marubuci, Steve Rosenberg
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Russia editor

Ka kwatanta kanka a matsayin Vladimir Putin.

Ƙasashen yamma suna maka ƙiyayya saboda ƙaddamar da yaƙi a Ukraine. Sannan an ƙaƙaba maka wasu takunkumi domin hana tattalin arzikin ƙasarka takaɓus a kasuwannin duniya.

Sannan kotun manyan laifuka ta bayar da umarnin a kama ka da zarar ka bar ƙasarka.

Ta yaya ne za ka iya nuna wa ƙasashen nan ƙwanji? sai kawai ka gwada shirya wani babban taro.

A wannan makon, shugaban ƙasa Putin zai gana da shugabannin ƙasashe 20 a birnin Kazan, a babban taron ƙungiyar ƙasashe maso haɓakar tattalin arziki wato Brics. Daga cikin jagororin ƙasashen da ya gayyata har da shugaban ƙasar China Xi Jinping, Firaiministan Narendra Moda da shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian.

Fadar gwamnatin Rasha ta ce wannan na cikin manyan taruka da aka taɓa yi a ƙasar Rasha.

“Wannan na nuna cewa yunƙurin daƙile Rasha ya samu tsaiko,” in ji Chris Weafer, ɗaya daga cikin jagororin cibiyar Macro-Advisory.

“Rasha za ta amfani da taron domin nuna ƙwanji da kuma jure takunkumin. Mun san akwai matsaloli a ƙarƙashin ƙasa, amma a zahiri, Rasha tana da ƙawaye, kuma ba za su gushe ba suna ƙawance da ita.”

Su wane ne ƙawayen Rasha?

Brics na nufin Brazil da Rasha da India da China da Afirka ta Kudu. Ƙasashen, waɗanda ake kira da masu nuna wa ƙasashen yammacin duniya yatsa a tattalin arziki, yanzu ƙungiyar ta samu ƙarin wasu ƙasashe kamar Masar da Ethiopia da Iran da UAE.

Haka kuma an gayyaci ƙasar Saudiyya domin shiga ƙungiyar.

Ƙasashen ƙungiyar Brics ne suke da kashi 45 na mutanen duniya. Ƙasashen da aka ƙara a ƙungiyar suna da arzikin sama da dala triliyan 28.5 (£22tn). Wato kusan kashi 28 na arzikin duniya.

Banar taron Brics na 2024 a birnin Kazan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Taron ƙungiyar ƙasashen Brics ɗin na bana zai wakana ne a birnin Kazan na Rasha

Hukumomi a ƙasar Rasha sun ce wasu ƙasashen guda 30 sun bayyana sha’awarsu ta shiga ƙungiyar Brics, ko kuma sha’awar ƙulla alaƙa da ƙungiyar. Wasu daga cikin ƙasashen ma za su halarci taron.

Amma bayan yunƙurin Vladimir Putin na nuna ƙwanji, wace nasara ake tunanin samu daga taron?

Domin rage ƙarfin takunkumin ƙasashen yamma, shugaban na Rasha zai yi yunƙurin fahimtar da ƙasashen ƙungiyar su fara mayar da hankali kan wani kuɗin daban wajen gudanar da hada-hadarsu ta duniya maimakon yawan amfani da dala.

“Yawancin matsalolin da tattalin arzikin Rasha ke fuskanta suna da alaƙa da hada-hadar kasuwanci, kuma yawanci suna da alaƙa da dalar Amurka,” in ji Mr Weafer.

“Babban burin Rasha shi ne rage kaka-gidan da dalar Amurka take yi a harkokin kasuwancin duniya. Tana so ƙungiyar ƙasashen na Brics su nemo hanyoyin gudanar da hada-hadarsu ba tare da rataya a kan dala ko fam ko wani ƙudin na ƙasashen G7 domin rage kaifin takunkumin da aka ƙaƙaba wa Rasha.”

Sai dai wasu suna ganin akwai lauje cikin naɗin na Brics, “idan aka duba da kyau, ƙasashen yamma za su yi farin ciki saboda China da India ba za su riƙa amincewa da buƙatun juna ba,” in ji Jim O’Neill, tsohon shugaban sashen tattalin arziki na Goldman Sachs.

“China da India ba su cika ga maciji ba, don haka samun haɗin kansu a fuskar tattalin arziki zai yi wahala.”

Ƙasashen masu haɓakar tattalin arziki suna so ne su ja daga da ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki wato G7 (Canada, Faransa da Jamsu da Italiya da Japan da Burtaniya da Amurka).

Ba China da India ba ne ƙadai suka da saɓani, akwai saɓani tsakanin sababbin mambobin ƙungiyar, Masar da Ethiopia, sannan duk alamun sauƙi da ake gani, akwai jiƙaƙiya tsakanin Iran da Saudiyya.

Sannan a daidai lokacin da Rasha take yunƙurin assasa wani sabon tsari a duniya, wasu ƙasashen Brics kamar India suna da burin cigaba da tattalin alaƙarsu mai kyau.

A birnin Kazan, Vladimir Putin zai so ya bayyana wa duniya alamar haɗin kai, sannan ya bayyana wa duniya cewa Rasha tana ƙwanjin jure wariyar ƙasashen yamma.