Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, By Andrew Webb
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Bayan ya fice daga neman takarar shugabancin Amurka, Joe Biden ya mara wa mataimakiyarsa Kamala Harris baya don ta maye gurbinsa.
Har yanzu ba a zaɓeta ba a matsayin ‘yartakara a hukumance a jam’iyyar Democrat, amma idan ta yi nasarar cin zaɓen za ta zama mace ta farko shugabar Amurka kuma wadda ke da tsatson Indiya da ƙasar Jamaika.
Kuma za ta zama shugaba ta farko tun bayan Andrew Jackson – a 1829 – ‘yar ‘yan-cirani.
Ga wani nazari da muka yi game da ƙwarewar Kamala Harris a fannin alaƙa da ƙasashen duniya, da kuma irin ra’ayinta kan wasu lamurra na manufofin Amurka kan ƙasashen wajen.
Asalin hoton, Reuters
Ukraine
Ɗaya daga cikin manyan manufofin ƙasashen waje da Kamala Harris da kuma ‘yan jam’iyyar Republican za su samu saɓani a kai shi ne batun yaƙin Rasha da Ukraine.
Ra’ayin Trump kan yaƙin na tayar da hankalin ƙasashen da ke goyon bayan Ukraine.
Wasu ƙasashen Yamma na fargabar idan Trump ya ci zaɓen zai rage ƙarfin goyon bayan da Ukraine ɗin ke samu kuma ya ƙarfafa wa Rasha gwiwar ci gaba da samun nasara.
A bayyane, Harris ta goyi bayan matakan Biden na tura wa Ukraine makamai a yaƙin tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa ƙasar a 2022.
Ta jagoranci tawagar Amurka zuwa taron harkokin tsaro da aka yi a birnin Munich na Jamus a 2022, ‘yan makonni kafin motocin yaƙin Rasha su afka wa Ukraine ɗin.
A watan Yunin 2024, ta wakilci Amurka taron neman zaman lafiya a Ukraine da aka yi a Switzerland.
Asalin hoton, Getty Images
Sai dai kuma, a kowane lokaci tana tare da rakiyar jami’an da ke da ƙwarewa sosai a fannin ƙasashen waje, kamar Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken, da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan.
Kamala ba ta taɓa zuwa Ukraine ba, amma ta gana da shugaban ƙasar sau shida.
Asalin hoton, EPA
Fargabar da ƙasashen Yamma ke yi ita ce cewa Trump zai iya tilasta wa Ukraine ta haƙura da yankunan da Rasha ta ƙwace mata domin kawo ƙarshen yaƙin.
Rasha da Nato
Kamala Harris ta ci alwashin cewa Amurka ba za ta taɓa gazawa ba wajen cika alƙawuran da ta ɗauka game da ƙawancen ƙasashe na tsaro watau Nato – wanda ya ƙunshi ƙasashen Turai da kuma na Arewacin Amurka.
Ta sha sukar Mista Trump game da barazanar da ya dinga yi ta janye Amurka daga ƙawancen idan sauran ƙasashen suka gaza ba da aƙalla kashi biyu cikin 100 na jimillar arzikin da suke samu a cikin gida.
Trump ya ce zai ƙarfafa wa Rasha Nato gwiwar ta mamaye duk ƙasar Nato da ta ƙi biyan kashi biyun cikin 100 da ya kamata ta bayar.
“Indai har wani tsohon shugaban Amurka zai ce zai ba wa ɗan kama-karya damar mamaye ƙawayenmu kuma Amurka na kallo – babu wani shugaban Amurka a tarihi da ya taɓa sassauta wa shugaban na Rasha,” a cewar Kamala.
Asalin hoton, Reuters
Isra’ila da yaƙin Gaza
Kamala ta goyi bayan Isra’ila a fili, tana mai cewa ƙasar na da ‘yancin kare kanta daga Hamas bayan harin 7 ga watan Oktoban 2023.
“Ba za mu saka wani sharaɗi ba game da goyon bayan da muke bai wa Isra’ila wajen kare kan ta,” kamar yadda ta faɗa a Nuwamban 2023.
Amma wata ɗaya bayan haka, ta nuna kakkausar ra’ayi game da Isra’ila sama da na Biden da sauran jami’an gwamnatin Amurka, inda ta ce “an kashe Falasɗinawa masu yawa” a hare-haren Isra’ila kan Hamas a Gaza.
“Dole ne Isra’ila ta ƙara ƙaimi wajen kare rayukan fararen hula,” a cewarta.
Asalin hoton, Getty Images
Zuwa watan Maris na shekarar nan, bayan zanga-zanagr da ta karaɗe jami’o’in Amurka kan yaƙin na Gaza, Kamala ta ce “dole ne Isra’ila ta yawaita kayan agajin da ake shigarwa Gaza – babu wani uzuri”.
Mista Trump ya nuna goyon baya sosai ga Isra’ila a wa’adin mulkinsa na farko. Ya bayyana goyon bayan Amurka ga Isra’ila ta yi amfani da birnin Ƙudus a matsayin babban birninta lokacin da ya kai ziyara.
Sau biyu Kamala tana zuwa Gabas ta Tsakiya a matsayinta na mataimakiyar shugabar ƙasa, amma ba ta je Isra’ila ba – idan aka kwatanta da Trump wanda ya je yana kan mulki.
Asalin hoton, EPA
Nahiyar Amurka ta Tsakiya
Ɗaya daga cikin ayyukan Kamala a matsayinta na mataimakiyar shugabar ƙasa shi ne daƙile dalilan da ke jawo baƙin haure shiga ƙasar daga Mexico.
Mista Trump da sauran ‘yan Republican sun sha sukar ta kan batun, suna cewa ta gaza kare iyakokin ƙasar.
Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da wani ɗanjarida ya tambaye ta game da dalilin da ya sa ba ta taɓa kai ziyara kan iyakar Amurka da Mexico ba, amsar da ta bayar ta jawo mata tsokana daga ‘yan’dawa.
Kamala ta ce: “Kada ku zo. Kada ku zo. Amurka za ta cigaba da tabbatar da dokoki a kan iyakarta. Idan kuka zo iyakarmu, za a mayar da ku.”
Asalin hoton, Getty Images
Sai kuma ta kai ziyara kan iyakar lokacin da ta yi balaguro zuwa Texas a watan Yunin 2021.
Asalin hoton, Reuters
Daƙile baƙin haure daga Mexico babbar manufa ce ta Trump bayan da ya sha yin alƙawarin gina katanga a kan iyakar a 2016.
Rahotonni sun ce yawan baƙin hauren da ke shiga sun ƙara yawa sosai a 2021, 2022, 2023 – lokutan da Kamala ke kan mulki kenan.
Sun ragu a watan Yuni lokacin da Shugaba Biden ya saka hannu kan wani umarnin shugaban ƙasa da ya hana wasu da yawa neman mafaka a ƙasar.
Asalin hoton, EPA
China
Kamar Trump, Kamala na yawan sukar China. Amma ta fi mayar da hankali kan siyasa sama da kasuwanci – saɓanin Trump.
Ta zargi China da “tsangwamar” maƙwabtanta a Tekun Kudancin China.
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Reuters
Lokacin da Trump ya kai irin wannan ziyarar a 2019 ya tsallaka ɓangaren Koriya ta Arewa, inda ya gaisa da Kim Jong-un.
Ya kuma tattauna da Kim ɗin a Singapore.
Asalin hoton, EPA
Afirka da Gabas ta Tsakiya
A 2023, Kamala na cikin jami’an gwamnatin Amurka da suka ziyarci Afirka.
Yunƙurin na nufin aniyar gwamnatin Amurka na ƙara yauƙaka alaƙa da ƙasashen Afirka yayin da take fuskantar ƙalubale daga sauran manyan ƙasashen duniya kamar Rasha da China.
A watan Mayun 2024, ta sanar da shirin taimaka wa ƙasashen ninka yawan layin intanet da kashi 80 cikin 100 tsakanin al’ummarta.
Kazalika, Kamala na cikin tawagar da ke ƙoƙarin rage kaifin da Saudiyya ke yi a Yemen.
Lokacin da take sanata, Kamala ta hana sayar wa Saudiyya makamai saboda yaƙin da take yi a Yemen ɗin da kuma kisan ɗanjarida Jamal Khashoggi a Turkiyya.
Asalin hoton, Middle East Monitor handout via Reuters
‘Yancin ɗan’adam
Baya ga rage wa Saudiyya kayan aiki, Kamala ta goyi bayan kafa dokokin da za su taimaka wa kare haƙƙin ɗan’adam a wasu wuraren.
Ta goyi bayan dokar da za ta ba da damar tunawa da kisan ƙare-dangi a Armenia, lamarin da ke jawo cecekuce tsakaninta da Tukriyya wadda ƙawarta ce a ƙungiyar ƙawance ta Nato tsawon shekara 100.
Kamala ta kuma goya wa yunƙurin dakatar da Iran daga mallakar makamin nukilya a 2015.
Asalin hoton, Getty Images
Ta kuma yi tir da harin da Amurka ta kai lokacin gwamnatin Trump a 2020 da ya kashe janar ɗin Iran Qassem Soleimani a Syria.
Daga baya ma ta goyi bayan wani yunƙuri da bai yi nasara ba da ya so ya hana ci gaba da kai wa jagororin Iran hari.